Majalisar zartarwar ta tarayya ta amince da bayar da lasisi ga wasu sabbin jami’o’i masu zaman kansu 11 a fadin kasar nan.Â
Ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa shi ne ya shaida hakan bayan zaman majalisar zartarwa a ranar Litinin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Nazarin CGTN: Manufar Sanya Muradun Amurka Gaba Da Komai Na Lalata Dangantakar Dake Tsakaninta Da Turai
- Yadda Ake Ayyukan Gina Ababen More Rayuwa A Jihar ZamfaraÂ
Ministan ya ce jami’o’in sun samu nasarar tsallake matakan da hukumar kula da jami’o’i na kasa (NUC) ta gindaya.
Alausa ya yi bayanin cewa, duk da cewa majalisar zartarwa ta tarayya ta sanya wa sabbin jami’o’i masu zaman kansu takunkumi, wadanda aka amince da su, sun yi nisa wajen yin rajistarsu.
“Wadanda aka amince da su suna kan bin matakai daban-daban kuma wasu sun yi nisa zuwa yanzu,” ya yi bayani.
Ministan ya bayar da jerin sabbin jami’o’in da suka hada da jami’ar New City, Ayetoro, a Jihar Ogun, jami’ar Fortune, Igbotako, a Jihar Ondo, jami’ar Eranoba, Mabushi, jami’ar Minaret, Ikirun, Osun Anned, jami’ar Abubakar Toyin, Oke-Agba, a Jihar Kwara da kuma jami’ar Southern Atlantic, Uyo, a Jihar Akwa Ibom.
Sauran su ne jami’ar Lens, Ilemona a Jihar Kwara, jami’ar Monarch, Iyesi-Ota, Jihar Ogun, jami’ar Tonnie Iredia da za ta koyar da ilimin sadarwa a birnin Benin, jami’ar Isaac Balami Aeronautics and Management, a Jihar Lagos da kuma jami’ar Kebin Eze Mgbowo, ta Jihar Inugu.
A cewar Alausa, Shugaban kasa Bola Tinubu ya himmatu wajen kyautata harkokin ilimi da kyautata gine-gine a bangaren ilimi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp