Gwamnatin Tarayya ta amince da sabbin manufofin amfani da mota da ke kunshe a sabon Tsarin Bunkasa Masana’antar Kera Motoci ta Kasa Na 2023.
Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Otunba Niyi Adebayo ne ya gabatar da takardar ga Majalisar Zartarwa ta Tarayya da aka yi ranar Larabar nan.
Cikin wadanda suka halarci taron akwai DG, NADDC, Jelani Aliyu.
Hukumar ta NADDC ta bullo da sabon shirin da za a yi amfani da karfin tuwo wajen tabbatar da dorewar nasarorin da aka samu kawo yanzu a cikin masana’antar kera motoci ta Nijeriya.
Sabbin manufofin na NAIDP za su ba da dabarar samar da gasa wajen zuba jarin da ake bukata daga masana’antun kera motoci, inda masu saka hannun jari, masu tasowa,da duk masu ruwa da tsaki za su taka rawar ganin da ake bukata.
Sabbbin mnufofin na NAIDP da aka amince na da nufin ba da damar haɓaka adadin motocin da ke cikin gida, wanda ya kai kashi 40 cikin 100 na cikin gida, samun kashi 30% na motocin lantarki da ake samarwa a cikin gida, da kuma samar da ayyukan yi miliyan daya.