Daga karshe dai gwamnatin tarayya ta kawo karshen cece- kucen dinnan da aka dade ana yi dangane da lamarin na zuwa aikin yiwa kasa hidima/aikin bautar kasa na wadanda suka mallaki takardar ilimi na Babbar difiloma ta kasa (HND).
Ministan ilim, dakta.Olatunji Alausa, shi ne wanda ya bada wannan sanarwar ranar Alhanis ta makon daya gabata cewar sai dai wadanda suka zauna makaranta suka yi karatu har suka samu ita Babbar difiloma ta kasa, sune suka cancancita tafiya yiwa kasa hidima na Hukumar NYSC.
- Zulum Ya Yi Alƙawarin Gyara Sansanin NYSC Na Borno
- Bayan Kwana 22, Tsohon Shugaban NYSC Tsiga Ya Kuɓuta A Hannun Ƴan Bindiga
Hakan ya biyo bayan ba’asin da aka samu da aka kammala tattaunawar da aka dauki lokaci mai tsawo da Shugaban Hukumar yiwa kasa Hidima Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu wanda aka saboda a samu gano bakin tsaren matsalar data dade tana ciwa mutane Tuwo,a kwarya wata rashin bada izini ga wadanda suke da takardar kammala karatun Babbar difiloma ta kasa HNd ba ma kamar wadanda suka yi karamar difiloma ba tare da sun zauna a makaranta ba, wanda akan je makaranta saboda lacca daganan a dawo gida.
A watan Fabrairu na wannan shekarar LEAdERSHIP ta bada rahoton dalilin da yasa aka samu matsalar kan yadda Hukumar ta NYSC take bada dama ta tafiya yiwa kasa hidima.
Matsalar ta shafi wadanda suka mallaki HNd wadanda suka yi karatun karamar difiloma Nd ba tare da sun zauna makaranta ba, ta haka ne ka yi zanga- zanga domin nuna damuwa da kuma bukatar ayi adalci kan yadda ake tura wadanda suka kammala makaranta tsarin Bautar kasa ko kuma yiwa kasa hidima.
Yawancin wadanda suke da HNd basu samu damar tafiya aikin Yiwa kasa Hidima/Aikin Bautawa kasa wanda hakan ne kuma aka gay a kamata ayi masu adalci kan lamarin
Sai dai kuma irin ci gaban da aka samu ya kawo ko samar da wata matsala ta yadda wadanda suka yi karatun suka kammala a makaranta sai ta kasance wasu daga cikinsu basu samu damar tafiya aikinyiwa kasa hidima ba saboda irin karatun da suka yi.
Da yake bada ta shi gudunmawa darekatan lamurran ‘yan jaridu da hulda da jama’a ma’aikatar ilimi ta tarayya Boriowo Folasade, ya fitar da sanarwa wadda take tabbatar da gaskiyar lamarin na abubuwan da suka biyo bayan dukkan tarurrrukan da kuma ganawar da aka yi.
Sanarwa ta nuna cewa sabon matakin da aka dauka wani abin farincikine ga wadanda suka kammala karatun da ake samun Babbar difiloma ta kasa HNd wadanda a baya ba a basu damar tafiya wuararen da za su yiwa kasa hidima ba.
An ma bayyana cewar matakan da ma’aikatar ilimi ta tarayya ta dauka na tabbatar da cewar ana yin adalci ya kasance ana tafiya da kowa a lamarin ilimi na Nijeriya.
Su ma wadanda suka kammala karatun nasu ba irin na wadanda suka zauna a makaranta ba, suma za su iya je aikin yiwa kasa hidima na shekara daya da takwarorin su wadanda suka samu ko karatun da ya basu damar samun digiri suke yi.
Domin samu daukar mataki wanda ba’a vata lokaci ba an umarci Hukumar kula da ilimin daya shafi fasaha da kere- kere (NBTE)ta gaggauta samar da bayanai na wadanda suka kammala HNd domin tafiya harkar ta yi wa kasa hidama NYSC.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp