Sabon karamin ministan ilimi, Goodluck Opiah, ya bada tabbacin cewa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dukufa wajen ganin ta shawo kan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi tare da tabbatar da dalibai sun koma azuzuwan karatu kwanan nan.
Opiah ya bada tabbacin ne a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida a Owerri sa’ilin liyafar taya murna da abokansa suka shirya masa.
- Takarar Musulmi 2: Kiristoci Ba Za Su Zabi APC Ba – Dakta Hakeem
- Hatsarin Jirgin Ruwa: Fasinjoji 15 Sun Mutu
Ya ce, “Ina tabbatar muku gwamnati ba ta yi biris da yajin aikin ASUU ba. Tattaunawa da shawarwarin da yadda za a shawo kan matsalar dukka suna ci gaba da gudana kuma tabbas ana samun sakamako mai kyau.
“Ina fatan nan kusa kadan rashin jituwar da ke tsakanin ASUU da gwamnati za a shawo kansa domin yaranmu su samu damar komawa makaranta.”
Ya ce, kalubalen da suke jibge a sashen ilimi ba abu ne da ba za a yi wasa da su ba, don haka ne ya bada tabbacin cewa za su yi aiki kafada da kafada da babban Ministan ilimi, Adamu Adamu domin dakile matsalolin da suke akwai a bangaren ilimi.