Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin gaggawa na tura mutanen da suka jikkata a hatsarin fashewar tankar man fetur da ya faru a Suleja, Jihar Neja, daga Asibitin Suleja zuwa manyan asibitoci domin samun ingantacciyar kulawar lafiya cikin sauri.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai Suleja a ranar Lahadi.
- Tinubu Ya Himmatu Wajen Kammala Titin Abuja Zuwa Kano Cikin Watanni 14 – Minista
- TikTok Ya Dawo Aiki A Amurka Bayan Matakin Da Trump Ya Ɗauka
Idris ya jagoranci wata tawaga daga Gwamnatin Tarayya, ciki har da Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dr. Nentawe Yilwatda, domin tantance halin da ake ciki da kuma miƙa ta’aziyyarsu ga Gwamnatin Jihar Neja da mazauna yankin bisa hatsarin da ya faru a Dikko Junction.
“Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana cikin matuƙar jimami kan wannan mummunan al’amari. Ya umurce mu da mu zo nan don ganin halin da ake ciki. Mun zagaya ɗakin masu jinya, kuma mun ga waɗanda ke cikin mummunan hali. Muna nan ana duba su, amma abin takaici, ɗaya daga cikinsu ya rasu. Wannan shi ne mutum na takwas da ya rasu sakamakon wannan hatsari. Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da cewa an yi gaggawar tura waɗannan mutanen da suka jikkata zuwa manyan asibitoci,” inji Idris.
Ministan ya yaba da gaggawar Gwamnatin Jihar Neja wajen bayar da taimakon gaggawa ga waɗanda suka jikkata.
Yayin da yake bayyana damuwarsa kan yawaitar fashewar tankar man fetur a ƙasar, inda mutane sama da 265 suka rasa rayukansu a cikin watanni biyar, Idris ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Tinubu ya kafa kwamiti domin bincikar musabbabin faruwar waɗannan al’amura da kuma samar da mafita don hana faruwar hakan a gaba.
“Shugaban ƙasa yana cikin damuwa sosai game da abin da ya faru. Ya kafa kwamitin bincike na musamman don gano musabbabin waɗannan abubuwan. A cikin watanni biyar da suka gabata, mun fuskanci manyan haɗura huɗu: ɗaya tsakanin Ibadan da Ife, wani a Agaie, Jihar Neja, inda mutane 48 suka rasa rayukansu, wani kuma a Jihar Jigawa inda mutane 144 suka mutu, sannan wannan a Suleja inda kusan mutane 80 suka mutu. Idan aka haɗa yawan waɗanda suka rasa rayukansu, sama da mutane 265 ne suka mutu a irin waɗannan haɗurra.
“Kwamitin da aka kafa, wanda ya ƙunshi manyan ma’aikatu da hukumomi kamar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, NEMA, FRSC, NUPRC, da NARTO, zai binciki musabbabin haɗurran tare da bayar da shawarwari don hana sake faruwar su,” inji Idris.
Ministan ya ce, a bisa umarnin da Shugaban Ƙasa ya bayar kwanan nan, Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) za ta ƙara himma wajen wayar da kan jama’a kan haɗarin kwasan man fetur daga tankokin mai da suka yi hatsari domin hana aukuwar irin waɗannan al’amura nan gaba. Ya yi tir da wannan ɗabi’a, yana mai bayyana ta a matsayin abin da ba za a yarda da shi ba.
Tawagar ta fara kai ziyara ta jaje ga Sarkin Suleja, Alhaji Auwal Ibrahim, sannan ta ziyarci waɗanda suka jikkata a Asibitin Suleja da wurin da haɗarin ya faru.
Sauran waɗanda suka kasance a tawagar har da Daraktocin Janar na Gidan Talabijin na Nijeriya (NTA), Abdulhamid Dembos; Muryar Nijeriya (VON), Jibrin Baba Ndace; da Rediyon Tarayya na Nijeriya (FRCN), Mohammed Bulama.