Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti mai karfi domin lalubo bakin zaren matsalolin da suka addabi bangaren farashin kayyakin masarufi na bukatun yau da gobe.
Ministar kasafin kudi, tsare-tsaren tattalin arziki, Hajiya Zainab Ahmed, ita ce ta sanar da hakan a ranar Laraba biyo bayan fitowa daga zaman Majalisar zartaswar Nijeriya da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Ministar tana mai cewa, kwamitin ya bada shawarar a gaggauta shawo kan Matsalolin da suke janyo tashin gauron zabi na kayan masarufi a fadin kasar nan.
Ministar ta ce an yi wa kwamitin bayani yadda abubuwa suka yi tashin gwauron-zabo da kuma yadda za a kawo karshen matsalar.