Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta ba da cikakken goyon baya ga samar da wani shirin fim mai nuna tarihin shekaru 25 na mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Majalisar Tuntuɓa ta Jam’iyyun Siyasa, wato Inter-Party Advisory Council (IPAC), a ranar Juma’a a Abuja.
- Kalaman Lai Chin-te Na Shan Suka A Fadin Taiwan
- NPA Za Ta Yunkuro Don Zamanantar Da Ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya – Dantsoho
Daraktan Yaɗa Labarai a ma’aikatar, Dakta Suleiman Haruna,ya faɗa a takarda ga manema labarai cewa Idris ya bayyana fim ɗin, wanda IPAC ce ta yi tunanin a shirya shi, a matsayin muhimmin tarihin tafiyar da dimokiraɗiyyar Nijeriya ta yi a cikin shekaru 25 da suka gabata.
Ya ce fim ɗin tarihin zai nuna nasarori, ƙalubale, da darussan da aka koya a wannan tafiya.
Ya ce: “Na yi farin cikin ganin ƙoƙarin da IPAC da shugabannin ta suke yi wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya, musamman ta hanyar fim ɗin wanda zai zama wata muhimmiyar shaida ta tarihi, domin girmama jaruman siyasar ƙasar mu da kuma nuna jajircewar Nijeriya a harkar dimokiraɗiyya. A kan haka, Gwamnatin Tarayya, ta hannun Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, za ta goyi bayan shirya wannan fim na musamman.”
Ya jinjina wa IPAC kan jajircewar ta wajen cigaban dimokiraɗiyya tare da jaddada muhimmancin haɗin kan jam’iyyun siyasa bayan zaɓe domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da cigaba.
“Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana goyon bayan a yi gasa mai kyau a siyasa, domin dimokiraɗiyya tana bunƙasa ne idan ana samun hamayya mai ma’ana da haɗin kai bisa muradin ƙasa ba tare da la’akari da bambancin jam’iyyun siyasa ba,” inji Idris.
Ya ƙara da cewa ɗorewar tsarin dimokiraɗiyya tana buƙatar haɗin gwiwa daga kowane ɓangare.
Ya ce: “Jam’iyyun siyasa su ne ginshiƙin dimokiraɗiyya; kuma yayin da hamayya take da muhimmanci a lokacin zaɓe, dole ne mu haɗa kai bayan haka don gina ƙasar mu.
“Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda babban ɗan dimokiraɗiyya ne, yana mutunta gasa mai tsafta, amma yana kuma fifita haɗin kai da cigaban ƙasa.”
Shugaban IPAC na ƙasa, Honourable Yusuf Ɗantalle, ya ce shirin fim ɗin tarihin zai bayyana cigaban da aka samu a fannonin gina ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da haɗin kan al’umma.
Ɗantalle ya ce: “Fim ɗin, a matsayin wani muhimmin tarihin ƙasa, zai mayar da hankali kan matasa, musamman ‘yan zamani (Gen Z), domin ya zama wata hanyar ilmantarwa da haɗe kan ‘yan ƙasa kan tafiyar dimokiraɗiyyar Nijeriya. Fim ɗin zai ƙunshi fitattun jaruman Nollywood kuma za a shirya shi da na’urori na zamani domin ya dace da matakin inganci na duniya.”
Daga cikin shugabannin IPAC da suka halarci taron akwai Mataimakin Ciyaman ɗin IPAC na Ƙasa Dipo Olayokun, da memba a majalisar, Cif Dan Nwayanwu, da Sakatare na Ƙasa, Maxwell Mabudem.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp