Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta yi shirin kafa cibiyoyin kiwon shanu a dukkan yankuna shida na ƙasar nan.
Ƙaramin Ministan Noma, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana hakan a rana ta biyu ta taron tattaunawa tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa, da kuma nazarin rabin wa’adin mulkin Tinubu.
Taron, wanda Gidauniyar Ahmadu Bello ta shirya, yana gudana ne a Arewa House, a Kaduna.
A cewar ministan: “Aikin haɗin gwiwa da haɗin kai tsakanin Ma’aikatun Noma, Muhalli, Albarkatun Ruwa, Bunƙasa Kiwon Dabbobi da kuma Tattalin Arzikin Ruwa yana da matuƙar muhimmanci domin cika manufofin Ajandar Sabunta Fata.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp