Ministan Gona da Raya Karkara, Dakta Mohammad Abubakar, ya ce, ma’aikatarsa za ta tallafa wa yankin Arewa maso Gabas da magunguna rigakafin cututtukan dabbobi fiye da miliyan 2 kyauta.
Dakta Abubakar ya sanar da haka ne a ta hannun jami’in watsa labaransa, Mista Mohammed Gana, a takardar manema labarai da aka raba a Abuja ranar Juma’a.
- Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Jihar Yobe Da Ton 360 Na Kayan Abinci
- Gwamnatin Kaduna Ta Kaddamar Da Sabon Tsarin Karantarwa Ta Intanet
Ya ce, Ministan ya bayyana haka ne a taron shekarar 2022 na gangamin rigakafin cutuututkan dabbobi da aka yi a garin Dadinkowa, da ke karamar hukumar Yamaltu Deba ta Jihar Gombe.
Ministan ya samu wakilcin Darakta mai kula da cututtukan dabbobi na kasa, Dakta Maimuna Habib, ya ce, za a tallafa wa yankin da maganin rigakafi har guda miliyan 2 kyauta don yakar cututtukan da suka hada da ‘Contagious Bovine Pleuropneumonia (CBPP)’, ‘Foot and Mouth Disease (FMD)’, ‘Peste Des Petits Ruminants (PPR)’ da kuma cutar ‘Newcastle Disease (ND)’ da sauran cuttukar da suke saurin kashe dabbobi.
Ya kuma kara da cewa, kiwo na daya cikin manyan kafar rayuwar al’ummar Nijeriya inda fiye da kashi 70 na mutanen Nijeriya ke rayuwa ta hanyar kiwon dabbobi da sauran su, kuma babbar kafa ce ta samun nama ga ‘yan Nijeriya.
A jawabinsa, shugaban kungiyar Miyetti-Allah ta Jihar Gombe, Mallam Madibbo Yahaya, ya gode wa gwamnati a kan wannan shirin ya kuma yi alkawarin bayar da dukkan hadin kan da ake bukata don samun nasarar shirin, ya kuma ce tabbas wannan shirin zai kara wa Nijeriya kudaden shiga zai kuma bunkasa rayuwar al’ummar Fulani.