Mashawarci na musamman ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf kan harkokin tsangayu, Sheikh Musa Falaki ya bayyan kyakkyawan tanadin da sabuwar gwamnatin Kano take da shi na inganta tsarin makarantun allo da Islamiyyu a Jihar Kano, musamman batun tsaftar muhallin Karatu da ban dakunan zagayawa da shigar da ilimin zamani da sauransu.
Mashawarcin ya bayyana haka ne a lokacin wani taron manema labarai da ya gudanar a Kano.
- Gwamnoni Sun Mara Wa Matakin Tinubu Na Cire Tallafin Mai Baya
- Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana 12 Ga Watan Yuni, Ranar Hutu
Sheikh Falaki ya bayyana cewa tun kafin rantsar da Abba Kabir an shaida tsarin kyautata makarantun allo da Islamiyyu cikin kunshin abubuwan da yake fatan aiwatarwa idan Allah ya tabbatar da shi a matsayin gwamnan Jihar Kano.
Da yake tsokaci kan hukumar harkokin almajirai da gwamnatin tarayya ta kafa wacce aka damka ta a hannun Honarabul Sha’aban Ibrahim Sharada a matsayin babban sakatarenta, ya ce wannan mukami da aka yi wa wannan matashi wanda daman dan cikin gidan Alkur’ani hakkake za a samu biyan bukata.
Ya ja hankalin shugaban hukumar almajiran da a yi kokarin shigar da alarammomi na hakika cikin wannan tsari.
A cewasa, shigar da alarammomi masu tsangaya cikin harkokin wannan hukuma ne zai bayyana irin matsalolin da tsarin ke fama da shi, a lokaci guda kuma su za su fito da hanyoyin magance matsaloli.
Sannan ya bukaci masu ruwa da tsaki a harkar makarantun allo wadanda ke tare da almajirai a dunga yin amfani da shawarwarinsu domin zai tabbatar da nasarar hukumar.
Falaki ya bukaci alaranmomi da su ci gaba da yi wa gwamnatin Abba Kabir addu’o’in domin samun nasarar da ake fata.