Gwamnatin Adamawa ta ware Naira biliyan 2.4 domin biyan kudaden rajistar jarrabawar WAEC da NECO ga wadanda suka cancanta a jihar.
Sakataren yada labarai na Gwamna Ahmadu Fintiri, Humwashi Wonisikou ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a Yola ranar Litinin.
- Kungiyoyin Ma’aikatan Jami’o’i SSANU Da NASU Sun Janye Yajin Aikin Gargadi Da Suka Shiga
- Ɗaliban Kuriga 137 Muka Yi Nasarar Kuɓutarwa A Zamfara, Ba Ɗalibai 287 Ba— Sojoji
Ya ce, kudaden za a biya ne don yin jarrabawar kammala sakandare ta wannan shekara, inda ya ba da tabbacin cewa, shirin zai dore.
“Gwamnatinmu ta himmatu sosai kuma ta kuduri aniyar sauke nauyin biyan kudaden jarrabawa a kan iyaye,” in ji shi.
Mista Wonisikou ya ce, gwamnati ta kuma fitar da Naira miliyan 500 domin biyan alawus-alawus na ‘yan asalin jihar da ke karatu a manyan makarantu.