Kwanan baya, kafofin yada labaru na kasar Amurka sun ruwaito cewa, gwamnatin kasar tana nazarin soke yawan kudin kwastam da gwamnatin Trump ta dora kan kayayyakin da ake shigar da su kasar daga Sin, a kokarin sassauta matsin lambar da take fuskanta ta fuskar hauhawar farashin kaya da ta kafa tarihi sau da dama.
A ranar 5 ga wata, wasu kafofin yada labaru sun ruwaito wata majiyar na cewa, kila gwamnatin Biden za ta soke kudin kwastan kalilan, wato dalar Amurka biliyan 10, kwatankwacin 2.7% na dalar Amurka biliyan 370, wato darajar kayayyakin da ake shigar da su daga kasar Sin, kana an dora kudin kwastam da yawa kansu.
Sanin kowa ne cewa, ‘yan siyasar Amurka kullum su kan salwantar da moriyar kasarsu da moriyar kamfanoninsu da ma moriyar Amurkawa domin kiyaye moriyar kansu da samun kuri’u.
Haka kuma, gwamnatin Amurka ta kara dakatar da soke kudin kwastam kan kayayyakin da ake shigar da su daga kasar Sin, wanda ke nufin, an kara illata tattalin arzikin Amurkar.
A matsayinsu na mafiya karfin tattalin arziki a duniya, hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Amurka tana amfana musu duka, yayin da yin takara a tsakaninsu yake illata moriyarsu duka. Shaidu sun sha tabbatar da hakan.
Yayin da Amurka ta ta da yakin ciniki da kasar Sin, kasar Sin ta bayyana matsayinta a fili, wato a shirye take wajen yin shawarwari da Amurka, amma kuma ba ta tsoron yin takara da Amurka.
Ya zuwa yanzu dai Sin na ganin cewa, soke karin kudin kwastam kan dukkan kayayyakinta, yana amfanawa Sin da Amurka da ma duniya baki daya. (Tasallah Yuan)