Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya ƙaddamar da aikin gyare-gyare da sabunta ginin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi kan kuɗin da ya haura Naira biliyan bakwai. Aikin ya haɗa da inganta kayan aiki, ofisoshi, da kuma gina sabon ofishin hukumar kula da harkokin majalisa.
A bikin ƙaddamarwar da aka gudanar ranar Talata, Gwamna Bala ya bayyana cewa wannan gyara na cikin shirin gwamnatinsa na sauya fasalin birane da samar da muhalli mai kyau ga ma’aikata domin sauƙaƙa aikinsu. Ya ƙara da cewa tuni aka riga aka biya rabin kuɗin aikin domin tabbatar da cewa aikin ya kammala cikin lokaci.
- Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Doke Afrika Ta Kudu
- Bauchi Da Gombe Sun Koka Kan Jinkirin Aikin Haƙo Mai Na Kolmani
Kwamishinan gidaje da muhalli, Hon. Danlami Ahmed Kawule, ya ce aikin zai ƙunshi gyaran ɗakin zaman majalisar, ofisoshin mambobi, gina sabbin hanyoyin ruwa da wutar lantarki na Sola, da kuma gyara titunan cikin majalisar. Ya ce za su sa ido sosai don tabbatar da inganci da aiwatarwa akan lokaci.
Tun da farko, mambobin majalisar sun koma ofishin tsohon mataimakin gwamna domin ci gaba da aikinsu yayin da ake gudanar da gyaran. Gwamnan ya yabawa fahimtar da ke tsakaninsa da majalisar, yana mai cewa hakan ne ke bai wa gwamnati damar aiwatar da ayyukan ci gaba.
Kakakin Majalisar, Hon. Abubakar Y. Suleiman, ya nuna godiya bisa wannan ci gaba, yana mai cewa haɗin kai tsakanin majalisar zartarwa da majalisar dokoki na taka muhimmiyar rawa wajen kawo cigaba a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp