• English
  • Business News
Tuesday, July 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Gombe Ta Yi Albishir Ɗin Gina Babban Zangon Noma Da Kiwo Ɗauke Da Kasuwar Duniya A Jihar 

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
3 weeks ago
in Manyan Labarai
0
Gwamnatin Gombe Ta Yi Albishir Ɗin Gina Babban Zangon Noma Da Kiwo Ɗauke Da Kasuwar Duniya A Jihar 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A jiya Lahadi ne Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya karɓi baƙuncin Mai Martaba Sarkin Gombe Alh. (Dr.) Abubakar Shehu Abubakar III a bikin Hawan Sallah na gargajiya, wanda aka fi sani da Hawan Gidan Gwamnati, a gidan gwamnati da ke Gombe.

Bikin na shekara-shekara, wanda ya kasance tushen al’adar masarautar Gombe, ya samu halartar Mai Martaba Sarki tare da hakimai da ‘yan Majalisar Sarki da masu riƙe da sarautun gargajiya da kuma ɗaruruwan mahayan dawakai sanye da kayayyaki na alfarma, inda suka karrama gwamnan cikin salon baje kolin al’adu, da ke nuna haɗin kai da jagoranci, a wani ɓangare na bukukuwan Sallah na bana.

  • He Lifeng Zai Ziyarci Birtaniya Tare Da Halartar Taron Farko Na Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Amurka 
  • Ndume Ya Gargaɗi Tinubu Kan 2027: “An Taɓa Yi Wa Jonathan Irin Wannan”

Bikin na bana ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da Mataimakin Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya kuma mai kula da harkokin jin ƙai na majalisar a Nijeriya, Mista Mohammed Fall, ɗan ƙasar Senegal da ya zaɓi yin bikin sallarsa ta bana a Jihar Gombe, sakamakon yanayin zaman lafiya da kuma jagoranci nagari da al’ummar jihar ke samu.

Gombe

Labarai Masu Nasaba

Farfesa Haruna Musa Ya Lashe Zaɓen VC Na Jami’ar Bayero Ta Kano 

Sojoji Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda Yellow Danbokolo A Zamfara

Da ya ke jawabi a wajen bikin, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana matuƙar godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da ya albarkaci bikin da zaman lafiya da haɗin kan da ake samu a jihar.

Ya yabawa Sarkin bisa yadda yake ɗabbaƙa al’adar ta Sallah mai daraja da kuma bada shawarwari na hikima da goyon bayan masarauta ga gwamnatinsa a tsawon shekaru.

“Masarautar Gombe tana ci gaba da zama ginshikin bada goyon baya ga wannar gwamnati, ya Mai Martaba, jagoranci da shawarwarinka na uba suna taimakawa wajen tsara manufofi da ayyukanmu da dama, tare da tabbatar da cewa sun yi daidai da kima da muradin al’ummarmu,” in ji gwamnan.

Gombe

Ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba gwamnati za ta fara aikin gina zangon harkokin noma da kiwo mai faɗin hekta 184 wanda zai ƙunshi katafariyar mayanka ta zamani da babbar kasuwar dabbobi ta duniya, da kuma kasuwar hatsi ta ƙasa da ƙasa; dukkansu masu ƙunshe cikakkun kayan aiki na zamani waɗanda aka tsara don haɓaka tattalin arziƙi ta fannin noma, da haɓaka samar da wadataccen abinci, da kuma samar da ayyukan yi.

Gwamna Inuwa ya kuma bayyana wasu manyan ayyuka da za a gadarwa ƴan baya da ake gudanarwa ciki har da tashar ruwa ta kan tudu, sannan ya jaddada kudurinsa na kammala manyan ayyukan da gwamnatinsa ta fara da suka haɗa da; Sakatariyar Jiha ta Zamani, da Sabuwar Majalisar Dokoki, da Rukunin Ɓangaren Shari’a, da nufin kawo ƙarshen hayar ofisoshi na shekaru da dama da ma’aikatu, da hukumomin gwamnati ke yi.

A game aikin haƙo mai na Kolmani kuwa, gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ganin Jihar Gombe ta ci moriyar albarkatun ƙasa da aka gano a cikinta.

Ya kuma jaddada ci gaba da yin haɗin gwiwa da Jihar Bauchi da abokan huldar ci gaban ƙasa don gaggauta fara aikin haƙo man.

Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na bin doka da oda, inda ya buƙaci jama’a su riƙa kula da kayayyakin more rayuwar da gwamnati ta samar, tare da kiyaye su a matsayin dukiyar kowa na yau da gobe.

“Muna da cikakkiyar masaniya game da alhakin da ke wuyanmu. Ko da yake lokacin barinmu mulki ya kusato, ba za mu ja da baya ba. Manufarmu ita ce mu bar gadon da ƴan baya za su yi alfahari da shi,” in ji shi.

Tun farko a nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Gombe, Dr. Abubakar Shehu Abubakar, ya ce bikin na Sallah ba bikin Idi ne kawai ba, har ma da ziyarar nuna godiya ga Gwamna Inuwa Yahaya.

Ya bayyana nasarori da dama da gwamnatin da Inuwa ke jagoranta ta samu, da suka haɗa da ginawa da gyaran ajujuwa fiye da 3,000, da samar da Manyan Makarantu na Musamman (Mega Schools) guda biyar, da ɗebe yaran da basa zuwa makaranta daga tituna zuwa aji, da farfaɗo da asibitoci da faɗaɗa shirin samar da ruwan sha na Gombe.

Ya kuma yabawa gwamnan a fannin sayowa da rarraba tallafin takin zamani, da bunƙasa masana’antu, da samar da sansanin masana’antu na Muhammadu Buhari, da ayyukan daƙile zaizayar ƙasa, da samar da ababen more rayuwa da hanyoyin mota da kuma ƙoƙarin da yake yi na tabbatar da aikin haƙo mai na Kolmani.

Gombe

“An kafa madatsar ruwa ta Balanga a 1978 amma tun lokacin ba a amfani da ita yadda ya dace, amma Gwamna Inuwa tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin raya ƙasa suna aikin gina magudanun ruwa don bunƙasa noma da kuma aikin samar da wutar lantarki.

Sarkin ya bayyana shirin nan na samar da hanyar ratse ta Arewacin Gombe da kuma aikin katafariyar mayanka ta zamani da cewa wani shiri ne da ya dace da tsarin da zai kawo ƙarshen al’adar safarar dabbobi zuwa kasuwanni masu nisa a kudu.

A yayin hawan, an gudanar da gagarumin jerin gwanon dawakai mai kayatarwa, inda mahaya dawakai na gargajiya suka baje kolin nasu ado cikin kayayyaki kala-kala, wanda ya jawo hankulan mahalarta da dama.

A matsayin wani ɓangare na shagulgulan, Gwamna Inuwa Yahaya ya gabatar da wata kyauta ta musamman ta Goron Sallah) ga Sarkin, inda ya ƙara tabbatar da alakar dake tsakanin masarautun gargajiya da gwamnatin jihar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

He Lifeng Zai Ziyarci Birtaniya Tare Da Halartar Taron Farko Na Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Amurka 

Next Post

Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 9 A Jigawa

Related

Farfesa Haruna Musa Ya Lashe Zaɓen VC Na Jami’ar Bayero Ta Kano 
Manyan Labarai

Farfesa Haruna Musa Ya Lashe Zaɓen VC Na Jami’ar Bayero Ta Kano 

19 minutes ago
Sojoji Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda Yellow Danbokolo A Zamfara
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda Yellow Danbokolo A Zamfara

5 hours ago
Barau, Ganduje Da Wasu Sun Isa Madina Don Halartar Jana’izar Aminu Dantata
Manyan Labarai

Barau, Ganduje Da Wasu Sun Isa Madina Don Halartar Jana’izar Aminu Dantata

9 hours ago
Duk Da Farfadowar Darajar Naira, Tsadar Kaya Na Ci Gaba Da Lulawa Sama
Manyan Labarai

Faɗuwar Darajar Naira Ta Sa Bashin Nijeriya Ya Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 149

11 hours ago
Haɗakar Jam’iyyun Adawa Ba Ya Ɗaga Mana Hankali – Sabon Shugaban APC
Manyan Labarai

Haɗakar Jam’iyyun Adawa Ba Ya Ɗaga Mana Hankali – Sabon Shugaban APC

12 hours ago
Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa
Manyan Labarai

Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

23 hours ago
Next Post
Mutum 3 Sun Rasu, 15 Sun Jikkata A Wani Hadarin Mota A Hanyar Kano

Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 9 A Jigawa

LABARAI MASU NASABA

Farfesa Haruna Musa Ya Lashe Zaɓen VC Na Jami’ar Bayero Ta Kano 

Farfesa Haruna Musa Ya Lashe Zaɓen VC Na Jami’ar Bayero Ta Kano 

July 1, 2025
Fahimtar Sabon Tunani: Yadda Sin Ta Samu Bunkasa A Tarihi Ta Hanyar Juyin Juya Halin Da Take Yi Wa Kanta 

Fahimtar Sabon Tunani: Yadda Sin Ta Samu Bunkasa A Tarihi Ta Hanyar Juyin Juya Halin Da Take Yi Wa Kanta 

July 1, 2025
An Yi Bikin Kade-Kade Don Taya Murnar Cika Shekaru 104 Da Kafuwar JKS

An Yi Bikin Kade-Kade Don Taya Murnar Cika Shekaru 104 Da Kafuwar JKS

July 1, 2025
Ba Gaskiya Ba Ne: Ɓarayi Ba Su Sace Ɗan Uwan Gwamnan Zamfara Ba

Ba Gaskiya Ba Ne: Ɓarayi Ba Su Sace Ɗan Uwan Gwamnan Zamfara Ba

July 1, 2025
Uwargidan Gwamnan Kaduna Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Noma Ga Mata Manoma

Uwargidan Gwamnan Kaduna Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Noma Ga Mata Manoma

July 1, 2025
Sin Za Ta Gabatar Da Shagulgulan Al’adu Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasarar Yaki Da Zaluncin Japanawa

Sin Za Ta Gabatar Da Shagulgulan Al’adu Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasarar Yaki Da Zaluncin Japanawa

July 1, 2025
Xi Jinping Ya Jaddada Niyyar Gina Babbar Kasuwar Kasa Ta Bai Daya, Tare Da Raya Tattalin Arziki Na Teku Mai Inganci

Xi Jinping Ya Jaddada Niyyar Gina Babbar Kasuwar Kasa Ta Bai Daya, Tare Da Raya Tattalin Arziki Na Teku Mai Inganci

July 1, 2025
Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu 

Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu 

July 1, 2025
Sojoji Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda Yellow Danbokolo A Zamfara

Sojoji Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda Yellow Danbokolo A Zamfara

July 1, 2025
Manomi Ya Ceto Jaririya Da Aka Binne Da Ranta A Kebbi

Manomi Ya Ceto Jaririya Da Aka Binne Da Ranta A Kebbi

July 1, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.