Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa samar da ingantaccen kiwon lafiya mai rahusa ga jama’a ya kasance jigon kudurin gwamnatinsa, inda ya ce gwamnatinsa za ta dauki ma’aikatan lafiya 200.Â
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya karbar bakuncin jami’an kungiyar masana harhada magunguna ta Nijeriya (PSN) karkashin jagorancin, Farfesa Cyril Usifor, wadanda suka je jihar don kammala shirye-shiryen taronsu na kasa a Gombe.
- Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka Na Kara Haifar Da Da Mai Ido
- Ba Zan yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ba, Cewar Dikko Radda
Gwamna Inuwa wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya shaida wa bakin nasa cewa kawo yanzu gwamnatinsa ta dauki ma’aikatan lafiya 260 aiki, daga ciki har da masu harhada magunguna.
Ya ce gwamnatinsa ta samar da akalla karamin asibiti guda a kowace gunduma cikin gundumomi 114 na jihar.
Gwamnan ya kara da cewa baya ga gyaran asibitin kwararru na jihar, gwamnatinsa ta sake farfado da manyan asibitocin Kaltungo da Bajoga, yayin da aka gina wani sabo a Kumo don samar da ingantaccen kiwon lafiya mai rahusa ga jama’a tun daga tushe.
“Saboda karancin lokaci, wadannan kadan kenan daga cikin dimbin ayyukan da gwamnan Jihar Gombe ya aiwatar kuma har yanzu yana kan yi don kula da lafiyar al’umma”.
Tun farko a jawabinsa, shugaban kungiyar masana harkokin magungunan ta Nijeriya, Farfesa Cyril Usifor, ya ce sun zo Jihar Gombe ne don kammala shirye-shiryen babban taronsu na shekara-shekara da aka shirya gudanarwa a wannan wata.