Gwamnatin jihar Imo ta amince da daukar nauyin kula da lafiyar dukkan ma’aikatan jiharta a wani bangare na kokarin samar da ma’aikatan gwamnati ingantattu domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Gwamnan, Hope Uzodinma, ya kuma bada tabbacin karin girma ga ma’aikatan da ya kamata a yi musu karin, ya ce, za a bayyana sunayen ma’aikatan nan ba da jimawa ba.
A cewarsa, nan ba da jimawa ba za a fara daukar karin malamai da hukumar kula da ilimi ta jihar Imo (SEMB) ke bukata.
Shirin Inshorar Lafiyar Jama’a kyauta ga ma’aikatan jihar Imo sama da 47,000, da shirin karin girma ga wadanda suka cancanta a kara musu girma, da dai sauransu, su ne muhimman batutuwan da aka tattauna a taron wanda ya gudana tsakanin Gwamna Uzodimma da manyan ma’aikatan jihar ta Imo.