Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da maido da malaman firamare 1,288 da aka kora daga aiki a watan Yunin 2022 bayan kammala jarrabawar tantancewa.
Hajiya Hauwa Mohammed jami’ar hulda da jama’a ta hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna SUBEB ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Kaduna ranar Laraba.
Mohammed ta bayyana cewa Malamai 1,266 ne suka zana jarabawar tantancewar yayin da wasu 22 kuma aka cire su daga cikin tsarin biyan albashin gwamnati kan zargin da ake musu na rashin gaskiya.
Hukumar a watan Yunin 2022 ta kori malaman firamare 2,357 sabida gaza samun makin din da ake bukata yayin zana jarabawar tantancewar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp