Gwamnatin Jihar Katsina ta sake nanata aniyarta na tsara ayyukan hako ma’adanai a jihar. Ta ce ta yi hakan ne domin tabbatar da cewa abubuwa na tafiya yadda ya kamata da kuma bin tsarin doka.
Mataimakin gwamnan jihar, Malam Faruk Lawal Jobe ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci tawagar jami’an gwamnatin jiha domin gano wuraren da ake hako ma’adanai a Dabar Hajiya ta Ranfingora da ke karamar hukumar Danja.
- NAHCON Ta Sanar Da Kuɗin Kujerar Hajjin Bana Duk Da Hauhawar Farashin Dala
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 185, Sun Kama 212, Sun Ceto Mutane 71 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
Mataimakin gwamnan wanda aka yi masa bayanin rin gwala-gwalan da farar kasa da ke wurin, ya yi gargadin cewa duk wanda aka kama yana hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba za a gurfanar da shi a gaban kuliya.
Ya ce tun da farko gwamnatin jihar ta bukaci dukkanin masu hako ma’adanai a jihar da su mika takardunsu domin tantancewa.
Mataimakin gwamnan, wanda ya samu wasu al’ummar yankin suna hakar farar kasa, ya gano cewa sun bar wurin da suke hako gwala-gwalan suka komo wurin hakar farar kasa domin sun ji labarin zuwansa.
Da yake wa mataimakin gwamnan bayani, shugaban kungiyar masu hako ma’adanai da ke Danja, Dahiru Dankande ya ce, tuni ‘ya’yan kungiyar suka bar aikin hako ma’adanai a wurin biyo bayan karewar lasisinsu a shekarar 2017. Dahiru Dankande ya yi roko ga gwamnatin jihar ta samr da na’urori na zamani.