A ƙoƙarin Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani wajen bunƙasa sashen ma’adinai ya haifar da gano manyan ma’adinai irin su zinari da litium da tagulla a Jihar Kaduna.
Manajan Darakta na Kamfanin Harkokin Ma’adinai na Jihar Kaduna (KMDC), Injiniya Shuaibu Kabir Bello, ne ya bayyana hakan a yayin taron makon ma’adinai na Nijeriya ta 2025 da aka gudanar daga ranar 13 zuwa 15 ga Oktoba a Abuja.
- Ƙungiyoyin Ma’aikatan Jihar Kaduna Sun Yabawa Gwamna Sani Kan Amincewa Da Sabon Albashin Ma’aikata
- Yadda DSS Suka Kama Masu Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna
A cewarsa, an gano waɗannan ma’adinai ne a lokacin bincike a yankin Gidan Waya da ke ƙaramar hukumar Jema’a cikin Jihar Kaduna, inda aka gano adadin tan 97 na ma’adinai.
Injiniya Bello ya ƙara da cewa an gano ma’adinan ne ta hanyar kamfanin Kian Smith da haɗin gwiwar hukumar kula da ma’adani ta jihar da kuma kamfanin Anka Metals JƁ bayan shafe shekara biyu ana gudanar da bincike.
Manajan daraktan ya sanar da cewa hukumar kula da haƙar ma’adanai ta jihar ta ƙirƙiri wani sabon tsari wanda zai kasance zai kawo ci gaba da raya albarkatun ƙasa. Ya ce an kafa kwamitin fasaha domin lura da aikin haƙa da tabbatar da adadin ma’adinan da ake da su a jihar.
Ya ce Hukumar Binciken Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) za ta jagoranci kwamitin, domin ita ce ke da ikon tattara bayanan ma’adinai na ƙasa baki ɗaya.
“NGSA ta yaba da ƙoƙarin gwamnatin Jihar Kaduna bisa gaskiya da bayyana bayanai, tare da yin kira da a gudanar da binciken tabbatarwa mai zaman kansa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa wannan haɗin gwiwar zai ƙara goyon bayan masu zuba jari a sashen ma’adinai na Nijeriya, tare da faɗaɗa bayanan kimiyyar ƙasa, wanda zai taimaka wajen haɓɓaka tattalin arzikin ƙasa ta hanyar albarkatun ma’adananta.













