A ci gaba da kokarin ganin an saukaka wa alhazan jihar Kaduna gudanar da ayyukan aikin hajji cikin kwanciyar hankali, gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar da wani kwamiti mai mutum 8 wanda zai tabbatar da samar da masaukai, ciyarwa, sufuri, hidimomin Hadaya, da tantuna don amfanin alhazan Jihar.
Mataimakiyar gwamnan jihar, Dakta Hadiza Balarabe, a lokacin da take kaddamar da kwamitin a gidan gwamnatin jihar Kaduna a ranar Larabar da ta gabata, ta ce zaben mambobin kwamitin an yi shi ne bisa la’akari da kwarewa, kwazo, da jajircewarsu wajen ci gaban jihar Kaduna da kuma rayuwar al’ummarta baki daya.
- Muna Rokon Shugaba Tinubu Ya Hana Ministoci Tafiye-tafiye Zuwa Kasashen Waje – Akpabio
- Sanatocin Arewacin Nijeriya Sun Matsa Wa Tinubu Lamba Kan Sake Bude Iyakar Nijar
Dakta Balarabe ta bayyana cewa, gwamnatin jihar Kaduna ta san irin kalubalen da aka fuskanta a hajjin bara, wanda ya jefa alhazan cikin kunci da damuwa.
A cewarta, wannan hakki ne na gwamnatin ta hada gwiwa da hukumomi domin lalubo inda matsalar take kuma ta gyara kura-kuran da aka samu tare da samar da ingantaccen tsari wanda zai ba da fifiko ga jin dadin Alhazan.
Ta bayyana cewa, muhimman bangarorin da kwamitin zai fi mayar da hankali su ne: bukatar kulawa da himma musamman wajen samar da kyakkyawan wurin kwana, ciyarwa, sufuri, da tantuna.
“Ina son mika godiya ta musamman ga Sheikh Salisu Abubakar bisa yadda ya amince ya jagoranci kwamitin kula da aikin hajjin 2024. Allah (SAW) Ya saka muku da alkairi kan sadaukarwarku da kuke yi kan ci gaban Jiharmu mai daraja”. Inji Dakta Hadiza
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin, Sheikh Salisu Abubakar, wanda ya yaba wa Uba Sani bisa yadda ya yi musu kyakkyawan zato ya mika musu ragamar wannan aiki, ya yi alkawarin yin aiki tukuru domin cimma bukatun da gwamnatin ke nema.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Baba Ahmed Rufa’i, Imam Buhari, Maimuna Waziri, Aminu Kasimu, Farfesa Muhammadu Mustapha Gwadabe, AVM Muhammad Rabiu Dabo, da Ummakulsum Jibril Maigwari.