Gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar da wani kwamiti da zai sake tsugunar da al’ummomin da suka rasa matsugunansu a Kudancin Kaduna sakamakon matsalolin rashin tsaro.
Gwamnan jihar, Malam Uba Sani ne ya kaddamar da kwamitin a gidan gwamnati na Sir. Ibrahim Kashim da ke Kaduna.
- Ramadan: Sarkin Kano Ya Roƙi ‘Yan Kasuwa Da Su Taimaka Su Rage Farashin Kayan Abinci
- Gwamnati Katsina Ta Kashe Miliyan 50 Wajen Gyara Motocin ‘Yansanda 15
Dakta Hadiza Balarabe wacce za ta jagoranci kwamitin, ta bayyana cewa, gwamnati na sane da alhakin da ya rataya a wuyanta na ‘yan kasa da suka rasa muhallansu sakamakon kalubale daban-daban na rashin tsaro.
Mataimakiyar Gwamnan ta bayyana cewa, babban makasudin kwamitin shi ne, samar da ingantattun tsare-tsare don sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar da ke Kudancin Jihar Kaduna da kuma sama musu ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da walwala.
Sauran Mambobin kwamitin sun hada da babban sakatare na ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Kabiru Mai Nasibi; sakataren gwamnatin jihar, Dakta Sale Momale; Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Mista Samuel Aruwan; Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar, Mohammed Lawal Shehu; da dai sauransu.