Gwamnatin Jihar Kaduna tare da haɗin gwiwar hukumar ci gaban Afirka ta ƙungiyar tarayyar Afirka (AUDA–NEPAD) reshen Nijeriya, ta ƙaddamar da rabon kayan noma ga ƙananan manoma 400 a faɗin jihar.
Gwamnan jihar, Uba Sani ya sake tabbatar da ƙudirin gwamnatinsa na tallafa wa ƙananan manoma da kuma ƙarfafa yawan amfanin gona a duk faɗin jihar, inda ya jaddada cewa noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin jihar.
- Yadda DSS Suka Kama Masu Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna
- Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar
Taron, wanda aka gudanar da shi a gidan tarihi na Arewa House da ke Kaduna ya zama wani muhimmin mataki na ci gaba a ƙoƙarin gwamnatin jihar wajen sauya fasalin harkar noma. Gwamna Sani ya bayyana cewa wannan haɗin gwiwa na nuni da yadda gwamnatinsa ke mai da hankali kan ci gaban da ya shafi jama’a kai tsaye, tare da daidaita gina tattalin arzikin da kuma samar da wadataccen abinci mai ɗorewa da kuma haɗin kai.
“Ƙananan manoma su ne ginshiƙin tsarin nomanmu, saboda haka tallafa musu yana nufin ƙarfafa tattalin arziki, tabbatar da wadatar abinci, da kuma inganta rayuwar dubban iyalai.”
Gwamnan ya bayyana cewa a ƙarƙashin shugabancinsa, noma yana ci gaba da kasancewa a sahun gaba na ayyukan gwamnati, inda aka ware fiye da naira biliyan 10 domin ɓangaren noma a kasafin kuɗin shekarar 2025.
Ya ƙara da cewa Kaduna ita ce jihar da ta cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa a yarjejeniyar Malabo kan saka hannun jari a harkar noma.
Shugaban AUDA–NEPAD a Nijeriya, Honarabul Jabir Abdullahi Tsauni, ya yaba wa gwamnatin Jihar Kaduna bisa samar da kuɗaɗen haɗin gwiwa da suka bai wa shirin damar faɗaɗa zuwa dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar.
A cewar Tsauni, an horar da ƙanana manoma 345 kan kyawawan hanyoyin noma da kuma dabarun noma masu jituwa da yanayin sauyin yanayi, ciki har da noman lambu na gida irin su tumatir, barkono mai zaƙi, masara, wake, da waken soya.
Komashinan noma na Jihar Kaduna, Murtala Dabo, ya bayyana cewa wannan shiri ya nuna yadda Kaduna ke da niyyar mayar da noma a matsayin sana’ar da ke kawo riba, ba kawai hanyar rayuwa ba.













