Gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya bayar da tabbaci ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC wajen yaki da cin hanci da rashawa a jihar.
Mai magana da yawun hukumar ta ICPC, Misis Azuka Ogugua, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja, ranar Alhamis.
- Ranar Tunawa Da Jarumai: Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Gidauniyar Tallafawa Iyalan Sojojin Da suka Rasu
- Gwamna Abba Yusuf Ya Nada Sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnati
Ogugua ta bayyana cewa gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da shugabannin hukumar karkashin jagorancin shugaban hukumar ta ICPC Dr. Musa Aliyu (SAN), suka kai masa ziyarar a Kano.
Ta ce gwamnan ya samu wakilcin mataimakinsa, Kwamred Aminu Gwarzo.
Gwamnan ya nuna jin dadinsa da ziyarar tare da yabawa nadin da shugaban na ICPC da shugaba Bola Tinubu ya yi masa kan kwazonsa d jajircewarsa kan aiki.
Ya kuma yabawa gwamnati kan yadda ta samar da hanyoyi irin su ICPC da EFCC, inda ya ce hukumomin za su taimaka wajen dakile rashin hukunta masu hannu a cikin tsarin.