Rahotanni na nuni da cewa, gwamnatin jihar Kano na shirin mayar da babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa kan mukaminsa wanda ya yi murabus a ranar Juma’a.
Jaridar Daily Trust ta samo cewa, an aika Majalisar Malamai ta jihar tare da wata tawaga ta manyan malaman addinin Musulunci domin su gana da Daurawa kuma su lallashe shi.
Hakazalika, wata majiya mai tushe ta shaida cewa, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Falgore da Babban Limamin Masallacin kasa na Abuja, Sheikh Ibrahim Maqari, duk suna daga cikin wadanda gwamnati ta aika domin ganawa da Sheikh Daurawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp