Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe fiye da Naira biliyan daya ga Jami’ar Yusuf Maitama Sule (YUMSUK) da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote (ADUSTECH) Wudil domin biyan kudaden alawus na ma’aikatan jami’o’in.
Kwamishinan ilimi na manyan Makarantun jihar, Dakta Yusuf Ibrahim Kofarmata ne ya bayyana hakan a yayin taron hadin gwiwa karo na 3 da shugabannin manyan makarantu, hukumar bayar da tallafin karatu, da manyan ma’aikatar jami’o’in suka gabatar wanda aka gudanar a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano.
- Kotu Ta Umarci Gwamnatin Tarayya Ta Biya Emefiele N100m Kan Tsare Shi Ba Bisa Ka’ida Ba.
- Gwamnan Kebbi Ya Rantsar Da Sabon Babban Alkali Da Shugabannin Manyan Makarantun Jihar
Ya ce, gwamnan ya amince da Naira miliyan 279 ga jami’ar YUMSUK don biyan alawus da kuma karin Naira miliyan 66 don yin taron yaye Dalibai na jami’ar.
Hakazalika, ADUSTECH, ta samu kason kudi fiye da Naira miliyan 629 domin biyan ma’aikatan kudin karin aiki da kuma Naira miliyan 38 na alawus ga Malaman jami’ar.