Gwamnatin jihar Kano ta amince da ranar Juma’a 28 ga watan Fabrairu, 2025 a matsayin ranar hutun zangon karatu na biyu ga dukkan makarantun sakandire na kwana da jeka-ka-dawo da kuma dukkan makarantun firamare a jihar.
Don haka, an bukaci Dalibai a makarantun da su koma gida gaban iyayensu a ranar Juma’a 28 ga Fabrairu, 2025.
- Sin Ta Jaddada Kudurin Hadin Gwiwa Da Kasa Da Kasa Kan Hakkin Dan Adam
- Ana Zargin Mourinho Da Furta Kalaman Batanci Akan Galatasaray
Wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar ta bayyana cewa daliban makarantun kwana da daliban za su komo makarantunsu a ranar Lahadi 6 ga Afrilu 2025.
Har ila yau, kwamishinan ma’aikatar Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda ya bukaci iyaye da daliban makarantun da su tabbatar sun koma makaranta a ranar da aka ware.
Ya yi gargadin cewa, za a dau matakin ladabtarwa a kan Daliban da suka gaza bin doka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp