Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da cire Naira 370 na kowane wata daga albashi da fansho na ma’aikatan gwamnatin jihar.
Sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Baffa Bichi a wata takarda da ya aikewa daukacin shugabannin hukumomin a ranar Litinin wacce Daily Trust ta gani a ranar Talata ta ce, an dakatar da cire kudaden nan take har sai an kammala bincike kan tsarin.
Gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ce ta kaddamar da wannan tsarin wanda ake zuba kudaden da aka cire a asusun wani kamfani mai suna Share Benefit Investment Limited.
Sakataren ya kara da cewa, sanarwar tana da muhimmanci sosai ga shugaban hukumomi da ma’aikatun gwamnatin don isar da sanarwar ga daukacin ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho a cikin jihar.
Daily Trust ta rahoto cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin bincikar gwamnatin da ya gada. Tuni dai, gwamnan ya fara rusa gine-ginen da ya ce haramtattu ne a jihar.