Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da wasu sabbin dokokin kare muhalli da nufin magance yawaitar gurɓata muhalli a fadin jihar.
Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi a jihar, Dakta Dahir Hashim ne ya bayyana hakan jim kadan bayan mika sabbin dokokin tsarin ga sakataren gwamnatin jihar, Umar Farouk Ibrahim, wanda ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon bayan gwamnati don aiwatar da tsarin.
- Abinda Ya Kamata Kusani Akan Wasan Barcelona Da Borrusia Dortmund
- Gwamna Zulum Ya Yi Allah-wadai Da Sabbin Hare-haren Boko Haram Da Sace-sacen Mutane A Borno
“Wadannan dokokin an tsara su ne musamman don magance matsalolin muhalli masu mahimmanci kamar fitar da sinadarai masu cutarwa, zubar da shara ba a inda ya dace ba, bahaya a bainar jama’a da kan tituna, da sakin gurbataccen ruwan masana’antu,” in ji Dokta Hashim.
Domin tabbatar da bin bin doka da oda a tsakanin al’umma, ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta ce za ta fara wani gangamin wayar da kan jama’a na tsawon mako takwas.
A cewar kwamishinan, gangamin zai mayar da hankali ne wajen wayar da al’umma, masana’antu, da sauran masu ruwa da tsaki kan sabbin dokokin da kuma muhimmancin kiyaye muhalli mai tsafta.
Ya kuma sanar da cewa, za a fitar da dokokin a cikin harsunan Hausa da Ingilishi a cikin mako guda domin inganta yanayin fahimtar dokokin a tsakanin al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp