Hukumar Tace Fina-finai da ÆŠab’i ta Jihar Kano, ta haramta shirya fim É—in da ke nuna fadan daba da harkar daudu a jihar.
Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne, ya bayyana hakan a yau jim kadan bayan wata tattaunawa da ya yi da masu shirya fina-finan Kannywood, suka hada da kungiyoyin MOPPAN, AREWA FILMS MAKERS, DIRECTORS da kuma PRODUCERS.
- Buhari Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Shugaban NLC, Ali Chiroma
- Gwamnatin Tarayya Ta Kara Kudin Wutar Lantarki A NijeriyaÂ
Shugaban ya ce biyo bayan Æ™orafe-Æ™orafen da al’umma k eyi a kan shirya fina-finan da ke nuna fadan daba da harkar daudu a Jihar Kano, ya bayar da umarnin dakatarwa tare da hana dukkan fina-finan da ke nuna fadan daba da harkar daudu a faÉ—in jihar.
Ya ce doka ce ta bai wa hukumar damar dakatarwa ko hana duk wani fim da ta ke ganin ya ci karo da tarbiyya tare da al’adar al’ummar jihar.
Ya ce lokaci ya wuce da za a sanya ido ana shirya irin wannan gurbatattun fina-finai da ke kokarin lalata tarbiyyar yara.
Wannan mataki da hukumar ta ɗauka dai yana da alaƙa da rikicin faɗan daba da ake fama da shi a unguwar Ɗorayi da ke Jihar Kano, inda a cikin wannan watan Ramadan aka kashe mutane da dama a unguwar.
Wasu a jihar sun koka kan ganin kallon fina-finan da suke nuna faÉ—an daba wajen taka muhimmiyar rawa wajen karuwar fadace-fadacen daba a jihar.