Gwamnatin jihar Kano ta haramtawa ‘Yan Adaidaita Sahu bin manyan Titunan jihar Kano daga Ranar Laraba 30 ga watan Nuwambar, 2022.
Gwamnatin ta ɗauki matakin ne biyo bayan samar da manyan motocin sufuri da za su dinga ɗaukar mutane a titinan da aka haramtawa matuka Adaidaita Sahun bin su.
- Dokar Adaidaita Sahu A Kano: Za Mu Kama Duk Wanda Ya Karya Doka – ‘Yan Sanda
- Gwamnatin Kano Ta Hana Sana’ar Adaidaita Bayan Karfe 10 Na Dare
Sanarwar haramcin ta fito daga Kakakin Hundunar kula da zirga-zirgar kula da ababen hawa ta Jihar Kano (KAROTA), Nabilisi Abubakar Kofar Na’isa, ta bayyana cewa an haramta wa matuka Baburan Adaidaita Sahun bin titinan Ahmadu Bello zuwa gabar Munduɓawa zuwa titin garin Gezawa da titin Tal’udu zuwa Gwarzo.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa ta tanadi manyan motocin sufuri domin sauƙaƙawa al’uma bin waɗannan hanyoyi, nan kuma ba da jimawa ba zata sanara da ragowar hanyoyin da aka haramta wa matukan bi da zarar shirye-shirye sun kammala.