Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin da zai binciki haramtattun gine-ginen da aka gina ba tare da bin ka’ida ko amincewa ba.
Manajan daraktan hukumar tsare-tsare da raya birane ta jihar Kano, Arch. Ibrahim Yakub Adamu, ne ya kwaddamar da kwamitin a dakin taro na hukumar, ya kuma nuna damuwarsa kan yadda aka gididdiba filaye da sayar da su a jihar ba tare da samun izinin gwamnati ba.
- Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Ciyar Da Abinci A Watan Ramadan
- Jami’ar Bayero Kano Za Ta Karrama Sanata Barau Da Adesina Da Digirin Girmamawa
Adamu ya yi gargadin cewa gwamnati za ta dauki matakin da ya dace a kan masu kunnen kashi da karya doka.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar KNUPDA, Bahijja Mallam Kabara, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa, Arch Adamu ya ce kokarin daukar wannan matakin ya zo daidai da manufar gwamnatin Kano ta Abba Kabir Yusuf na ganin Kano ta zama ta daya a kasar nan a fannin tsara birane.
Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Jami’in tsara birane, Junaid Abdullahi, yayin da sauran membobin kwamitin sun hada da dukkan daraktoci da wakilan kamfanoni masu zaman kansu a jihar.
Arch Abdullahi ya bukaci jama’a da su rika tuntubar masu unguwanni da masu ruwa da tsaki kafin su sayi duk wani fili a ko’ina a fadin jihar.