Hon Umar Haruna Doguwa, kwamishinan ilimin jahar Kano ya wakilci mai girma gwamnan jihar Kano, H.E Alhaji Abba Kabir Yusuf wajen maida daliban Jihar Borno zuwa garin Maiduguri bayan kammala karatunsu a Jihar Kano.
Lokacin tsohon Gwamnan Kano,  Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya dauko wadannan yara daga sassan Jihar Borno sakamakon rikichin Boko Haram da ya yi sanadiyyar rasuwar iyayensu, ya gina musu makaranta a Jihar Kano, “School of IDP Mariri” wanda suka kammala karatunsu a wannan shekarar ta 2023.
- Za A Fuskanci Karancin Motoci A Nijeriya Sakamakon Karin Haraji
- NPA Ta Gargadi Masu Jibge Kwantaina Ba Bisa Ka’ida Ba
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ta hannun sakataren gwamnatin jihar, Honarabul Dakata Bukar Tijjani ya karbi wadannan daliban.
Gwamnan, ya godewa Gwamnatin Jihar Kano bisa gudunmuwarsu akan ci gaban Jihar Borno.
Akwai kwamishinonin ilimi, mata, addinai da na noma na Jihar Borno a wajen bikin.
Dalibai 23 ne cikinsu 200 suka kammala wannan makaranta da kakkyawan sakamako, a cikinsu akwai mutum 49 da suka haddace Al-kur’ani mai girma.
Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin ci gaba da daukar nauyin karatun wadannan dalibai har jami’a domin kara dankon zumunci Jihar Kano da Borno.