Gwamnatin jihar Kano ta umarci dukkan ma’aikatan jihar da su tantance albashinsu na watan Maris kafin a biya su.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Ibrahim Faruk ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa ranar Litinin.
- Ba A Taɓa Shugaban Ƙasar Da Ya Kai Mahaifina A Nijeriya Ba – Ɗan Shugaba Tinubu
- An Cafke Wadanda Ake Zargi Da Daba Wa Dan Wasan Nijeriya Mazaunin Kasar Ireland Wuka Har Lahira
Ya bayyana cewa, an dauki matakin ne a matsayin don magance korafe-korafen da ma’aikatan suka yi na rashin daidaito a Albashinsu na watan Janairu da Fabrairu.
“Za a lika sunayen tare da albashin ma’aikata a wurare masu mahimmanci a cikin harabar ma’aikatu, ofisoshin gwamnati da sakatariyar kananan hukumomi 44 na jihar don sauƙaƙe aikin,” in ji Faruk.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp