Gwamnatin jihar Kano ta lashi takobin gabatar da takardar korafi akan mai shari’a Benson Anya, daya daga cikin Alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar.
Ta bayyana hakan ne bisa kalaman cin zarafi da ta yi ikirarin Anya ya furta akan jami’iyyar NNPP da kuma magoya bayan Kwankwasiyya.
- Gwamna Yusuf Ya Mika Wa Majalisar Kano Ƙaramin Kasafin Kuɗin Sama Da Naira Biliyan 50
- Duk Da Hukuncin Kotu, Gwamna Yusuf Ya Amince Da Kashe Naira Biliyan 3 Kan Ayyuka
A makon da ya gabata ne, kotun ta yanke hukuncin cewa, gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP, bashi ne wanda ya lashe zaben gwamnan jihar ba.
A jawabinsa kan hukuncin kotun, Anya ya bayyana cewa, Magoya bayan Gwamna Yusuf, masu tada rikici ne da ke kokarin cin zarafin bangaren Shari’a.
Kazalika, ya danganta magoya bayan NNPP a matsayin masu sanya jar Hula, masu tayar da rikici, ‘yan kungiyar asiri, ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga kuma wadanda suka ji zafin shan kaye, wanda hakan ya sa suka yi wa rayuwar Alkalan kotun barazana.
Sai dai, a martanin da kwamishinan yada labarai na jihar, Baba Halilu Dantiye ya mayar akan kalaman na Anya, ya yi nuni da cewa, kalaman batanci na Anya ba wai kawai ya yi sune akan jar Hula ba, a’a, har a akan marigayi Malam Aminu Kano wanda a lokacin rayuwarsa, ya kasance akan gaba wajen sa jar Hula.