Gwamnatin jihar Kano ta gana da shugabannin ‘yan bangar siyasa da suka tuba a jihar tare da yi musu alkawarin tallafa musu ta hanyar sauya tunaninsu da horar da su sana’o’i da kuma kayan aikin fara sana’ar.
Taron wanda ya gudana a ranar Talata a Kano ya samu halartar tubabbun ‘yan barandan siyasa da masu satar waya kusan 718.
- Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Kwangilar Hanyoyi 17 Akan Naira Biliyan 40.8
- Sin Ta Gabatar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakaninta Da Amurka A Stockholm
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Waiya ya yi kira ga mahalarta taron da su rungumi tuba da gaskiya tare da bayar da hadin kai ga shirin gwamnati na sauya rayuwarsu.
“An shirya tsaf, kawai jira ake ‘yansanda da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta dauki bayananku.
“Waɗannan matakai ne masu mahimmanci waɗanda ta hanyarsu za ku zaɓi irin sana’ar da kuke son koya kuma za a horar da ku duk irin sana’ar da kuka zaba, daga karshe a gwangwajeku da kayan aikin fara sana’ar,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp