Majalisar gudanarwar kasar Sin, wato gwamnatin kasar ta zartas da wata ka’ida kan sanya ido sosai kan jama’a masu karamin karfi, da taimakon rukunonin al’umma, da shirye-shiryen ba da taimakon abinci ga tsoffi da kuma aiwatar da doka dangane da ‘yancin mallakar fasaha.
A cewar taron majalisar gudanarwar kasar wanda firaministan gwamnatin kasar Mr. Li Qiang ya jagoranta, ya kamata a yi kokarin ganin an samar da aikin ba da taimako ga jama’a yadda ya kamata, cikin sauri da inganci, don ganin an kyautata rayuwar jama’a. (Ibrahim Yaya)