Gwamnatin Jihar Katsina ta gabatar da matsayinta a taron jin ra’ayoyin jama’a na yankin arewa maso yamma kan gyaran kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999.
Taron jin ra’ayoyin jama’ar na shiyyar arewa maso yamma, wanda kwamitin majalissar dattawa kan gyaran kundin tsarin mulki ya shirya, ya gudana ne a dakin taro na otel ɗin Bristol Palace Hotel da ke Kano.
Shugaban kwamitin Jihar Katsina kan gyaran kundin tsari mulki, Sanata Ibrahim Ida, ya gabatar da takardar matsayar jihar a madadin Gwamna Malam ɗikko Umar Raɗda.
- An Yanke Wa Mai Gadi Da Mai Dafa Abinci Hukuncin Kisa Kan Kashe Tsohon Kwamishina A Katsina
- Gwamnatin Katsina Ta Fara Bayar Da Maganin Zazzabi Kyauta A Asibitoci
Sanata Ibrahim, yayin da yake bayani kan abubuwa da ke cikin takardar matsayar, ya ce Jihar Katsina na goyon bayan muhimman ɓangarori da aka tsara domin a yi gyara a kundin tsarin mulki.
Ya ce jihar na goyon bayan cin gashi kai na ƙananan hukumomi, sake fasalin shari’a, tsarin shugabanci na hada kai da dukkan jama’a, batun tsaro da ƙarƙirar ƴansanda jihohi.
A cewar shugaban kwamitin, Katsina na kuma goyon bayan batun sauke wasu ikon gwamnati daga matakin tarayya zuwa jihohi, saka sarakunan gargajiya a cikin kundin tsarin mulki da kuma sake fasalin harkokin kuɗi.
Sanata Ibrahim ya shaida wa kwamitin cewa an tattara dukkan ra’ayoyi da buƙatun jama’ar Katsina, tare da gabatar da su a cikin takardar matsayar.
Tun da farko, yayin da yake ƙaddamar da taron jin ra’ayoyin jama’a, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan gyaran kudin tsarin mulki ya buƙaci a riƙa yin irin wannan taron lokaci zuwa lokaci domin ya dace da halin da ake ciki.
Sanata Barau Jibrin, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawa, ya tabbatar da cewa dukkan abubuwan da aka tattara daga gwamnati, ƙungiyoyi da jama’a za a gabatar da su a gaban majalisar domin yin doguwar tattaunawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp