Gwamnatin Jihar Katsina ta sha alwashin kare iyakokin burtali da kuma dauki matakan kan cin labi-labi da manoma ke yi a wasu bangarori na jihar.
Sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Barista Abdullahi Garba Faskari ya bayyana hakan lokacin da ya ziyarci dajin Jaudi a mazabar Karofi ta karamar hukumar Dutsin-Ma.
- Yadda Na Kirkiro ‘Brain-chip’ Da Ke Dawo Wa Wadanda Aka Haifa Da Makanta Ganinsu – Elon Musk
- FIFA Ta Dakatar Da Eto’o Zuwa Kallon Wasanni Har Tsawon Watanni Shida
Ziyarar ta biyo bayan korafin da makiyayan yankin suka yi na cewa manoma sun mamaye inda za su rika kiwon dabbobinsu a yankin.
A madadin makiyayan yankin, shugaban kungiyar Miyetti Allah na garin Karofi, Bello Mamma Fulani ya yi korafin cewa an mamaye musu wurin kiwo ba bisa ka’ida ba.
Sakataren gwamnatin jihar ya bayyana irin muhimmancin da makiyayan da manoman suke da shi wajen maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakaninsu domin cimma nasarar da aka sanya a gaba.
Ya kara da cewa wannan gwamnati tana yin duk mai yiyuwa wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, musamman manoma da makiyaya.
A jawabinsa, shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Dutsin-Ma, Sada Ibrahim ya ce karamar hukumar tana mara wa kokarin gwamnati baya wajen tabbatar da ganin makiyaya da manoma sun zauna lafiya a yankin.