Gwamtin Jihar Katsina ta jaddada aniyarta na bullo da jarrabawar gwaji ga ma’aikata domin tabbatarwa da bayar da dama ga masu kwazo su jagoranci aikin gwamnati da samar da damar samun horo ga ‘ya’yan talakawa a kasashen ketare.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin wakilan tsaffin daliban kwalejin ilimi ta Kafanchan ‘yan she-kara ta 1997 a wata ziyara da suka kai masa.
- Binciken CGTN Ya Nuna Yadda Masu Bayyana Ra’ayoyi Suka Zargi Nuna Fin Karfi Da Amurka Ta Yi A Harkokin Intanet
- Gwamnatin Tarayya Ita Kadai Ba Za Ta Iya Daukar Dawainiyar Kudaden Ilimi Ba – Minista
Gwamnan ya ce ta hanyar haka ne kawai gwamnatin jiha za ta tabbatar da bayar da dama ga dukkan rukunin jama’a ba tare da la’akari da asali ba.
Ya tunatar da cewa manyan sakatarori ne rukuni na farko da suka rubuta wannan jarrabawa ta gwaji kafin a ba su damar ci gaba da zama a mukaman da suke a kai.
Gwamna Radda ya kara da cewa yin hakan ya kara ba da dama ga wasu sabbi domin darewa kan sabon mukamin babban sakatare.
Ya ce daukar malaman makaranta da aka yi a kwanan nan da daukar nauyin kara-tun dalibai a kasar Misra an yi su ne bayan gudanar da jarrabawar gwaji.
A cewarsa, gwamnatinsa ta wajabta cewa yaran da suka kammala sakandiren gwamnati kadai ne za a bai wa damar zuwa kasar wajen domin samun horo.
Tun farko da yake jawabi, shugaban tsoffin daliban kwalejin, Farfesa Salihu Garba Kargi ya ce ziyarar na da nufin taya gwamna murna a matsayinsa na daya daga ci-kinsu ya samu damar zama gwamna tare da tattaunawa da shi kan tsare-tsare domin karramashi.