Gwamnan jihar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Sule yayi kira ga sabon Shugaban Kungiyar Shugabanin kananan hukumomi na kasa da ya daukaka darajar jihar Nasarawa a idon yan Nijeriya.
Gwamna Abdullahi Sule, yace samun wannan Babban Mukami ci gaba ne so sai da ya shafi duk wani dan jihar Nasarawa.
- Kotu Ta Tsare Wani Mutum Kan Yi Wa ‘Yar Shekaru 11 Ciki A Legas
- CBN Ya Kara Adadin Kudin Ruwa Zuwa Kashi 24.75
Yin amfani da kwarewa da nuna dattako da gaskiya, da adalci da rikon amana zai kara daga darajar al’ummar jihar Nasarawa a idon ‘yan Nijeriya.
Gwamnan yayi farin ciki da Shugaban Karamar hukumar Lafia Wanda shi ne a yanzun aka zaba a matsayin Shugaban kananan hukumomin Nijeriya.
Gwamna Abdullahi Sule ya yabawa sabon Shugaban, Alhaji Aminu Ma’azu Mai fata.
Ya kuma roke shi ya ci gaba da nuna dattako da wakilci na gari kamar yadda ya saba ga al’umman jihar Nasarawa.