Gwamnatin jihar Nasarawa ta gargadi masu amfani da sinadarai wajen kamun kifi acikin ruwa da su daina, in ba haka ba za su fuskanci hukunci idan aka kama su.
Kwamishinan Ruwa da Ci gaban karkara na jihar, Mohammed Muluku, bayyana hakan, inda ya kara da cewa, zuba sinadari acikin ruwa domin kamun kifi yana da hadari. Domin al’umma suna amfani da ruwan domin sha da ayyukan gida.
- Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
- ‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio
Sinadarin kan janyo asarar rayuka ta hanyar haifar da cututtuka bayan al’umma sun yi amfani da ruwan.
Kwamishinan, ya bayyana cewa gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule ta gina rijiyar burtsatse 200 a sassa daban-daban na ƙananan hukumomi 13 na jihar cikin shekara biyu da suka gabata.
Muluku ya bayyana hakan ne a ranar Talata a babban birnin jihar Lafiya, yayin wani taron bayar da rahoton ma’aikatu da Kwamishinan Bayanai, Al’adu da Yawon Bude Ido, Dr. Ibrahim Tanko, ya shirya domin bai wa jami’an gwamnati damar bayyana nasarorinsu.
Kwamishinan ya ce wannan yunkuri na cikin ƙoƙarin gwamna Sule na inganta samun ruwan sha mai tsafta da haɓaka ci gaban karkara a fadin jihar.
Ya bayyana cewa gwamnati ta kuma gyara burtsatse 300 a kauyuka da birane domin rage matsalar ƙarancin ruwa da kuma ƙara wa jama’a damar samun ruwan sha mai tsafta.
Muluku ya ƙara da cewa, akwai gidan ruwa fiye da tara (9) a Awe, Obi, Keana, Lafia, Nassarawa-Eggon, Akwanga, Wamba, Nasarawa da Toto, kuma dukkansu gwamnati tana kula da su a halin yanzu.
Ya ce gwamnati ta bayar da ayyukan tono da tsaftace gidajen ruwa, tare da shirin gina sababbi domin biyan bukatar sababbin unguwanni da suka taso.
Sai dai kwamishinan ya koka da cewa, akwai matsaloli da ke hana samun cikakken ruwan sha mai tsafta, kamar lalata kayan aiki da satar igiyoyin wutar lantarki da famfo daga wasu ɓata-gari.