Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ayyana hutun kwanaki biyu – Alhamis da Juma’a – don zaɓen ƙananan hukumomi da za a yi a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa tuni gwamnan ya bai wa dukkan waɗanda aka naɗa a maƙaman siyasa hutun mako guda su koma mazaɓunsu don yin kamfen, da kuma tabbatar da Jam’iyyar APC ta samu nasara a yankunansu.
- Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba
- An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi
Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Alhaji Abubakar Usman, ya ce an ayyana Alhamis, 30 ga Oktoba da Juma’a, 31 ga Oktoba, 2025 a matsayin ranakun hutun aiki a duk faɗin jihar.
Ya ce, an ɗauki wannan matakin ne don bai wa masu zaɓe a faɗin jihar damar gudanar da zaɓen da ke tafe a jihar.
Ya ƙara da bayyana cewa, Gwamna Bago ya umarci dukkan hukumomin tsaro a Jihar da su tabbatar an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da tsari, yana mai sake tabbatar da alƙawarin gwamnatin Jihar na tabbatar da tsarin zaɓe mai aminci da kwanciyar hankali.














