Hukumar kula da harkokin addini ta jihar Neja ta karyata rahotannin da ake yaɗawa na cewa, ta sanya dokar hana wa’azin addinin musulunci a jihar, tare da bayyana ikirarin da kafafen sada zumunta ke yaɗawa a matsayin labaran “kawar da hankulan jama’a daga gaskiyar labari.”
Mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga Babban Daraktan Hukumar, Amb. Haruna Mustapha (Dago), ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
- Sin Ta Gano Wani Dutse Mai Sassaka Na Daular Qin A Kan Tsaunin Qinghai-Tibet
- Lauyoyi Biyu Sun Janye Daga Kai Jaafar Jaafar Ƙara, Sun Ce An Sanya Sunayensu Ba Bisa Ƙa’ida Ba
Shugaban kungiyar Kiristocin Arewacin Nijeriya (CAN), Rabaran John Hayab, ya kuma yi kira da a hada kai da kuma bayar da sahihin rahoto.
Rahoton rashin fahimtar da aka fara yadawar, ya biyo bayan taron kwamitin zaman lafiya da kwantar da tarzoma na jihar, wanda Darakta Janar ya jagoranta a ranar 4 ga watan Satumba.
Rashin fahimtar sahihin sakamakon taron ya sa wasu suka rahoto cewa, kwamitin ya dakatar da Malamai daga yin wa’azi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar ba ta da hurumin haramtawa Malaman Addinin Musulunci yin wa’azi sai dai in ya bayyana a fili an taka ƙa’idojin hukumar da ta shimfiɗa”.
A cewar Hukumar, an kira taron ne domin gabatar da fom din rijistar yin wa’azi ko Da’awah da kuma bin tsarin tantancewa.
Ta bayyana shirin a matsayin wani yunkuri na wayar da kan jama’a don “hana rashin fahimtar juna da kuma daƙile yaɗuwar wa’azin yaudara” a faɗin jihar Neja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp