Kungiyar kare hakkin Musulmi a Nijeriya (MURIC), ta koka kan shirin da Gwamna Ahmed Aliyu na Jihar Sakkwato ke yi na zargin tsige Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.
Babban Daraktan MURIC, Farfesa Isiaq Akintola ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
- Gwamnan Sakkwato Ya Ba wa Ma’aikata Kyautar Dubu Talatin Goron Sallah
- An Ceto Mutane 250 Daga Hannun ‘Yan Ta’adda A Sakkwato
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta yamutsa hazo da cece-kuce kan tsige sarakuna biyar a jihar Kano.
A baya dai Gwamna Aliyu ya kori hakimai kusan 15 bisa zarginsu da aikata wasu laifuka.
A cikin kunshin sanarwar, Akintola ya ce Musulmin Nijeriya ba za su amince da duk wani yunkuri na tsige Sarkin Musulmin ba.