Gwamnatin jihar Sakkwato ta siyawa ‘yan gudun hijira gidan din-din na Naira miliyan 100 a cikin birnin jihar domin inganta jin daɗi da walwalarsu.
Kwamishinan yaɗa labarai, Sambo Bello Danchadi ya bayyana cewar sabon muhallin ya kasance mazaunin da ‘yan gudun hijira suke zaune tsawon shekaru a bisa kulawar wani mutum mai zaman kansa.
- Mun Rage Tasirin ‘Yan Bindiga A Kebbi Da Zamfara – Sojoji
- Lakurawa Sun Kashe ’Yan Sa-kai 13 A Wani Sabon Hari A Kebbi
Danchadi wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a ƙarshen taron majalisar zartarwar gwamnatin jiha a ranar Laraba ya ce majalisar ta tattauna sosai a bisa ga buƙatar sayar da gidan da mamallakinsa ya gabatar ga gwamnati.
Kwamishinan ya bayyana cewar gidan mallakin gwamnati zai kasance na ‘yan gudun hijira a yanzu da nan gaba wanda hakan zai taimakawa kokarin da gwamnati ke yi wajen gane ‘yan gudun hijirar da kuma tallafa masu yadda ya kamata.
A tsayin shekaru dai ɗumbin al’umma sun rasa rayuka da dukiyoyinsu a dalilin hare- haren ta’addanci da ‘yan bindiga suka ɗauki tsayin lokaci suna kaiwa a Gabacin Sakkwato wanda ya tilastawa jama’a da dama ƙauracewa garuruwa da muhallansu domin tsira da rai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp