Gwamnatin jihar Sokoto za ta kashe naira miliyan 998 a shirin ciyar da al’umma buda baki a watan Ramadan da ke tafe.
Za a gudanar da ciyarwar ne a cibiyoyin buda baki 155 da ke fadin jihar wadanda aka kara daga 130 a shekarar da ta gabata domin saukaka wa jama’a gudanar da ibadar Azumi cikin sauki.
- Sanata Natasha Za Ta Fuskanci Hukunci Daga Kwamitin Ɗa’a Na Majalisa
- Ministar Wajen Madagascar: Muna Godiya Ga Tawagogin Likitanci Na Sin
A jawabinsa a wajen kaddamar da rarraba kayan abinci ga cibiyoyin buda baki, Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana cewa, za a bai wa kowace cibiya kayan abinci da kayan girki.
Ya ce an zabi mutane 1, 400 da za su gudanar da aikin wadanda daga ciki mata 610 ne za su rika girka abincin, sannan ana kyautata tsammanin mutum 20,000 ne za su amfana da abincin a kullum a kowace cibiya har zuwa karshen Azumin bana.
Gwamnan ya bukaci shugabannin cibiyoyin da su gudanar da aikin a bisa gaskiya da adalci, haka ma ya bukaci al’umma su kasance cikin natsuwa a yayin rabon abincin
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp