Gwamnatin tarayya na aiki tukuru domin kasar nan ta fara kera magunguna a cikin gida nan ba da dadewa ba, in ji babbar sakatariyar ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta tarayya, Kachollom Daju.
Daju ta bayyana haka ne a Abuja a yayin wani taron karramawa na masu sana’a da aka shirya mata, biyo bayan karramawa ta duniya da kwalejin koyar da harhada magunguna ta Afirka ta Yamma ta yi mata.
- Jirgin Sama Ya Yi Hatsari A Sama, Mutum 1 Ya Mutu 30 Sun Jikkata
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 40, Sun Kone Gidaje Da Dama A Filato
Ta ce, ma’aikatar tana aiki tare da duk masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya don samar da ingantattun ayyuka, samar da kiwon lafiya ga duniya baki daya da kuma bude hanyoyin da za a tabbatar da samar da kayayyakin da kasar nan ke bukata a cikin gida.
Babban sakataren kwalejin koyar da magunguna ta Afirka ta Yamma, Farfesa Ibrahim Adekunle Oreagba, ya ce, karramawar da aka yi wa Daju, yawanci ana bai wa mambobin kungiyar da suka kasance shugabanni a kasashen da suke.