Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani taron karawa juna sani na kwanaki biyu a jihar Kano domin haɓaka aikin ma’aikatan jin ɗaɗin jama’a da kayan aikin da ake bukata domin magance kalubale daban-daban na zamantakewa da na Jinƙai.
Taron wanda Ma’aikatar Agaji da Rage Talauci ta Tarayya ta shirya tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Mata, Yara da Nakasassu ta Jihar Kano, an shirya shi ne domin inganta kwarewar ma’aikatan jin dadin jama’a don magance matsalolin da suka hada da talauci, cin zarafin mata, kare yara, da kuma matsalolin Jinƙai.
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 157, Sun Ƙwato Bindigu Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano
- Hadin Gwiwar Kasashen Asiya Da Afirka Na Habaka Karfinsu Na Dogaro Da Kai Da Cin Moriya Tare
Da yake bude taron, babban sakatare na ma’aikatar Jinƙai da rage raɗaɗin talauci a ma’aikatar tarayya, Dakta Yakubu Adam Kofarmata, ya ce shirin ya kara jaddada kudirin gwamnati na karfafa tsarin jin dadin jama’a, da karfafawa al’umma gwiwa, da inganta rayuwa ga ‘yan Nijeriya masu rauni.
Shima da yake jawabi a wajen taron, kwamishinan harkokin mata, yara da nakasassu na jihar Kano, wanda daraktan gudanarwa, Alhaji Mohammed Sambo Iliyasu ya wakilta, ya jaddada goyon bayan jihar kan ci gaban harkokin inganta zamantakewa da walwalar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp