Gwamnatin tarayya ta baiwa gwamnatin jihar Kano tallafin tireloli na shinkafa 100 da tirela 44 na dawa da kuma tirela na masara guda hudu domin rabawa mabukata.
Sakataren yada labarai na gwamnan Kano, Sanusi Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Lahadi a Kano.
- Gwamnatin Nijeriya Ta Yaba Da Ƙwazon Tawagar ‘Yan Nijeriya A Wasannin Afirka
- Ba Za Mu Lamunci Amfani Da Yunwa A Matsayin Makamin Yaki A Gaza Ba – Tarayyar Turai
Tofa ya kara da cewa, gidauniyar Dangote ta kuma tallafa wa jihar da buhunan shinkafa 120,000 mai nauyin kilo 10.
“Bayan wannan tallafin, gwamnatin jihar Kano ta raba tireloli 145 na hatsi iri daban-daban domin rabawa a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar,” inji shi.
Tofa ya ce, an samu nasarar aiwatar da wannan shiri ne tare da hadin gwiwar kananan hukumomin jihar.