Gamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata, 1 ga Oktoba, 2024, a matsayin ranar hutu domin bikin murnar samun ‘yancin ƙasa da kuma cikar Nijeriya shekaru 64 da samun ‘yanci.
Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya.
- Jami’ar Franco-British International Ta Shirya Soma Aiki A Watan Oktoba – Shugaban Jami’ar
- KANSIEC Ta Sauya Lokacin Zaben Kananan Hukumomin Kano Zuwa Oktoba
Sannan kuma ya taya ‘yan Nijeriya na gida da waje murnar zagayowar wannan rana.
Sanarwar mai dauke da sa hannun babban sakatare a ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, ta yaba wa al’ummar Nijeriya saboda sadaukarwa da kuma juriya da nuna kwazo har zuwa wannan lokacin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp